100+ Hausa Proverbs (Karin Magana) Full of Wisdom

100+ Hausa Proverbs (Karin Magana) Full of Wisdom

Hausa Karin Magana, otherwise known as Hausa proverbs are very rich just like their English counterparts. When you hear them, sometimes you wonder how the people that originated them came up with them. They are so full of wisdom as they encompass proverbs on all facets of life.

However, in this piece, we will be limiting ourselves to the ones purely on wisdom. Thus;

112 Karin Magana Full of Wisdom

  1. Ganin zumar wani, kada ta sa ka zubar da madacinka.
  2. Ganyen doka daya ya fi na dorowa dari.
  3. Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, shi ya kwana bai runtsa ba.
  4. Duk wanda aka gani da tabarma, yana neman wurin shinfida ne.
  5. Duk wanda yayi noma ya huta da awo.
  6. Duk zafin tukunya dole a sauke.
  7. Duk zurfin ruwa akwai yashi a ciki.
  8. Duk tashin tsuntsu, sai sama ta ga bayan shi.
  9. Dutsen tsakiyar ruwa bai san ana rana ba.
  10. Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba.
  11. Duk abinda ka gani a gidan sarki, ya na kasuwa.
  12. Durkusa wa wada ai ba gajiyawa ba ne.
  13. Duniya kamun kifi, kowa ya kamo ya sa a goransa.
  14. Don kai ake hula, har kunne ya samu.
  15. Dan banza yashi ne ko an dunkula shi baya dunkuluwa.
  16. Dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido.
  17. Dan kuka mai jawa uwarsa jifa.
  18. Dan kuka baya zama dan tsamiya Ciwon da kare yayi idan dan akuya ne sai wuka.
  19. Ci naka in ci nawa, ba rowa bane halin zama ne.
  20. Da yayyafi kogi kan cika.
  21. Da tsohuwar zuma ake magani.
  22. Da rarrafe yaro kan tashi.
  23. Da ruwan ciki ake jan na rijiya.
  24. Ciki da gaskiya wuka bata huda shi.
  25. Cin loma yafi jiran malmala.
  26. Barin kashi a ciki baya maganin yunwa.
  27. Biyan bukata yafi dogon buri.
  28. Babban goro sai magogin karfe.
  29. Barawon rakumi daga daddawa ya fara.
  30. Barewa baza ta yi gudu ba danta yayi ra
  31. Babban kaya sai gammo.
  32. Ba’a jan ragama da rigima.
  33. Bakin karen masoyi yafi farin ragon makiyi.
  34. Bakin tukunya mai fidda farin tuwo.
  35. Bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane.
  36. Ba’a maida hannun kyauta baya.
  37. Ba’a yanka karfe sai da karfe.
  38. Baka cin zamanin ka ka ci na wani.
  39. Ba’a kada miya tun dawa na rumbu.
  40. A rashin uwa ake uwar daki.
  41. Ayi wanda za’a yi bera ya zubar da garin kyanwa.
  42. Bani na kashe zomon ba rataya aka bani.
  43. Ba iya kwanciya aka fi kare ba sai dai abun rufa.
  44. Baka do gadon mutun amma kana da gadon batun sa.
  45. Ba ji ba gani auren kurma da makaho.
  46. Ba maraya sai rago.
  47. Ba’a fafe gora ranar tafiya.
  48. A rashin sani kaza ta kwana kan dami.
  49. Ana yi da kai yafi ba’a yi, sarki ya koma mai anguwa.
  50. Ba dan tsayi akan ga wata ba.
  51. Ba domin tuwo akayi ciki ba.
  52. Ana zaton wuta a makera, sai gashi a masaka.
  53. Annurin fuska kaurin hanji.
  54. Ana rabaka da kaya kana nade gammo.
  55. A ruwa ake dadewa ba a wuta ba.
  56. Ana sara ana duban bakin gatari.
  57. Ana bikin duniya ake na kiyama.
  58. Ana ganin wuyan biri ake daureshi a kwankwaso.
  59. A bakin tsoho goro kan tsufa.
  60. A bakin wawa ake jin Magana.
  61. Ba’a sarki biyu a gari daya.
  62. Ba’a shan zuma sai an sha harbi.
  63. Ba’a shan zuma sai da wuta.
  64. Ba’a sayan jaki don a ci sai don daukan kaya.
  65. Ba’a raina zakin gwandan daci don ba’a bata ruwa.
  66. Ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
  67. Ba’a sake wa tuwo suna.
  68. A bari ya huce shi ke kawo rabon wani.
  69. A bar kaza cikin gashinta.
  70. Abin bai dace ba, an ga Malami da gatari.
  71. Abinda babba ya gani a zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai gan shi ba.
  72. Allah Ya fishemu da hawa dokin zuciya.
  73. Abinda ruwan zafi ya dafa, in an hakura, ruwan sanyi ma saiya dafa.
  74. Abinda ya bata a duniya in an je lahira a ganshi.
  75. Abin da ya kori bera ya fada wuta, yafi wutar zafi.
  76. Abin da sake, an bai wa mai kaza kai.
  77. Abin da sake an bai wa mai rogo bawo.
  78. Abin da zuciya ya dauka, gangan jiki ma dole ya dauka.
  79. Abin da baki ya daura, hannu baya kwancewa.
  80. Abin mamaki, mai karfi na bara.
  81. Allah ke ci da maraya ko da mai uba bai so ba.
  82. Allah na taimokon wanda ya taimaki kanshi.
  83. Abokin cin mushe ba’a boye mashi wuka.
  84. Abin fada na mai baki ne.
  85. Abu a rufe mai raba zumunci.
  86. Abu kamar wasa, karamar Magana ta zama babba.
  87. Abu uku su ne maganin zaman duniya, tawakkali, dangana da hakuri.
  88. An daga sama anyi wa wada sata.
  89. Ana babbakar giwa wa ke ta zomo?
  90. Abu namu maganin a kwabe mu.
  91. Abokin kirki ya fi mugun dan uwa.
  92. A dade ana yi sai gaskiya.
  93. A dubi ruwa a dubi tsaki.
  94. Abokin sarki, sarki ne.
  95. Abokin kuka ake gaya wa mutuwa.
  96. A ci baa sayar ba, kwai ya fi doki.
  97. A ci a rage, shi ne ci.
  98. A jefar da kwallon mangwaro a huta da kuda.
  99. A aiki kare ya aiki wutsiya.
  100. Aiki da hankali yafi aiki da agogo.
  101. Aikin banza hutun jaki da kaya.
  102. A kan wanke tukunya domin tuwon gobe.
  103. Allah ke gyara tuwon makauniya har a ci ba kuda ba gashi.
  104. Allura a cikin ruwa mai hikima kan tsinta.
  105. Bari murna karen ka ya kama zaki.
  106. Bashi hanji ne yana cikin kowa.
  107. Allaura a cikin teku mai daukanta sai mai dace.
  108. Alheri gadon bacci ne.
  109. Alheri ne bakon gishiri a shekara ana lashewa.
  110. Alhaki kuykuyo ne mai shi yake bi.
  111. Amfanin sani aiki da shi.
  112. Ba za’a ci kwado da yaro ba sai ya wanke hannunsa.
  113. Da walakin goro a cikin miya.

Conclusion

The above Karin Magana (Hausa proverbs) are at your disposal. Feel free to use them anytime you feel like it. You could also tell us more in the comments section. Thank you.