100 Funny Hausa Proverbs (Karin Magana Guda 100)

100 Funny Hausa Proverbs (Karin Magana Guda 100)

Here are 100 Karin Magana (Karin Magana guda 100) that will get you rolling on the floor without even knowing because of laughter. You could even have your eyes full of tears because of the joy they carry along. Sit back, relax, and go through them one after the other.

If you loved them, then you will truly love these 100 pure Hausa proverbs (karin magana tsantsa)

A Collection of 100 Funny Hausa Proverbs (Karin Magana Guda 100)

  1. Abin ba dadi, mahaukaci ya tauna kasha.
  2. Kowa ya ci zomo ya ci gudu.
  3. Dan masara ana goyon ka kana gemu.
  4. Dama yaya lafiyar kura balle tayi hauka.
  5. Daminan bana ba kamar ta bara ba, kwado ya fada ruwan zafi.
  6. Da sauran tsalle an daura wa kwado garwashi.
  7. Da ganin dan kunama zai yi harbi.
  8. Abin da sake, an bai wa mai kaza kai.
  9. Abin da sake an bai wa mai rogo bawo.
  10. Da haka muka fara, kuturu yaga mai kyasbi.
  11. Da kyar na kai yafi da kyar aka kamani.
  12. Da na gaba ake gane zurfin ruwa.
  13. Da muguwar rawa, gwamma kin tashi.
  14. Da sanin ango aka yi wa ‘yan buki duka.
  15. Da sannu auduga zai zama zare.
  16. Da ganin kura kasan zata ci akuya.
  17. Kora da hali ya fi kora da sanda.
  18. Kowa ya hau motan kwadayi, a tashar wulakanci za’a sauke shi.
  19. Abin mamaki furar sayarwa a akushi.
  20. Abin mamaki kare da tallan tsire.
  21. Abin mamaki mai gari gwauro talaka da mata hudu.
  22. Abin mamaki matar falke ta haifi jaki.
  23. Abin nema ya samu, matar falke ta haifi jaki.
  24. Abin nema ya samu, matar dan sanda ta haifi barawo.
  25. Abin ya girma, kashe kwarkwata da tabarya.
  26. Abin rabo ne, kuturu ya kama tarwada.
  27. A daga sama an yi wa wada sata.
  28. Aikin banza jefa agwagwa a ruwa.
  29. Aikin banza zani da aljuhu.
  30. Aikin banza bille a ciki.
  31. Aikin banza talaka ya grime sarki.
  32. Aikin banza yin kiba a kunne.
  33. Aikin banza kiwon makahon kare.
  34. Aikin banza kare da gudun laya.
  35. Aikin banza sauri ba wurin zuwa.
  36. Aikin banza makaho da waiwaye.
  37. Aikin banza harara a duhu.
  38. Akuya ko bata haihuwa tafi kare.
  39. Allah Ya bamu lafiya baba yaga tsirara.
  40. Allah Ya tsare gatari ga noma.
  41. Allah Ya hada mu da mai son mu koda mugune.
  42. Allah Ya kawo kudi talauci ya ji kunya.
  43. Ana babbakar giwa wa ke ta zomo?
  44. Ana rabaka da kiwon akuya kana kyalla ta haihu.
  45. Ana son wawa, haihuwarsa ne ba’a so.
  46. Ana yabon ka sallah, ka kasa alwala.
  47. Anyi ba’a yi ba ba ance tsirkiyada fatan kunkuru.
  48. Arha cefane kunu daga ruwa sai tsamiya.
  49. Arha kamar jamfa a Jos.
  50. Arha maganin mai wayo.
  51. Iya yi ci-rani ba miji.
  52. Arha wanzami ya samu kan mai saiko.
  53. A rashin sani bako ya sha ruwan wanka.
  54. A ruwa ake dadewa ba a wuta ba.
  55. Arziki rigar kaya kana ja yana ja.
  56. Arziki rigar kaya ga dadi ga suka.
  57. An sha ruwan gwangwala a kara tsayi.
  58. “A yi abunda za’a yi” ramamme ya zagi maye.
  59. “Ba samun duniya ba” wurin da za’a zauna a ji shine injin dan tsako.
  60. Ba’a hada gudu da susan duwawu.
  61. Ba shiga ba fita an ba mahaukaciya tsaron kofa.
  62. Bako ba sallama wawa ne.
  63. Banga alama ba, ance wa kuturu ya gama lafiya.
  64. Banza a banza kare a karofi.
  65. Banza girman mahaukaci, karami mai hankali ya fishi.
  66. Ciwon da kare yayi idan dan akuya ne sai wuka.
  67. Dan banza yashi ne ko an dunkula shi baya dunkuluwa.
  68. Dole ne zuwa biki da muni.
  69. Don kai ake hula, har kunne ya samu.
  70. Duniya ba gaskiya, barawo ya rasa shaida.
  71. Duk daya ne, makaho yayi dare.
  72. Duk daya ne, mara sallah ya je gidan bamaguje.
  73. Duk tashin tsuntsu, sai sama ta ga bayan shi.
  74. Ga ni ga Allah barawo a hannun mata.
  75. Gwamma barnar ruwa da na wuta.
  76. Haka da nade-nade, dan wake ya ga tubani.
  77. Hakorin dariya shi ke cizo.
  78. Hauka dangi-dangi, kowa da irin nasa.
  79. Icen taba Allah na ruwa tana bushewa.
  80. Idan kai na da tsoka, kowa ya taba ya ji.
  81. In ba karamabani ba, me ya kai doki mahauta?
  82. In ana son ka da laifi, ko ruwa ka ashiga sai a ce ka tada kura.
  83. In ka na son sauri aiki yaro inda yake so.
  84. In maciji ya sari mutum, in ya ga tsumma sai ya gudu.
  85. In makaho yace a yi wasan jifa, ya taka dutse ne.
  86. “Jiki magayi” shan tabar mai koyo.
  87. Jin labarin gwani, ya fi ganin raggo.
  88. Ka so makiyinka, sai ya rasa mafita.
  89. Ka kiyayi furfura, ko da ta arne ce.
  90. Karshen lalacewa, namiji da guda.
  91. Karambanin bako a kori barawo ya kai gudummawa.
  92. Kidan jajibiri  baya tada hankalin kare.
  93. Komai dadin guda, ba a yi ma asara.
  94. Kowa da irin kiwon da ya karbe shi makwabcin mai akuya ya sayi kura.
  95. Komai ramar giwa ta fi kwando goma.
  96. Komai ya ji ban da barkono a ido.
  97. Kowa ya hadiye tabarya, ya kwana a tsaye.
  98. Kowa ya raina gajere bai taka kunama ba.
  99. Kowa ya goya kare ya san yadda zai yi da bakin.
  100. Maganin biri, karen maguzawa.
  101. Mai cinikin shan zuma, in reshe bai karye da shi ba, kwarya ta fashe masa.
  102. Ba ji ba gani auren kurma da makaho.

I hope you enjoyed reading this karin magana guda 100. I can trust you couldn’t help but laugh so hard. Tell us which among the karin magana guda 100 did you enjoy most in the comments section.

100 Funny Hausa Proverbs (Karin Magana Guda 100)

100+ Hausa Proverbs (Karin Magana) Full of Wisdom

Hausa Karin Magana, otherwise known as Hausa proverbs are very rich just like their English counterparts. When you hear them, sometimes you wonder how the people that originated them came up with them. They are so full of wisdom as they encompass proverbs on all facets of life.

However, in this piece, we will be limiting ourselves to the ones purely on wisdom. Thus;

112 Karin Magana Full of Wisdom

  1. Ganin zumar wani, kada ta sa ka zubar da madacinka.
  2. Ganyen doka daya ya fi na dorowa dari.
  3. Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, shi ya kwana bai runtsa ba.
  4. Duk wanda aka gani da tabarma, yana neman wurin shinfida ne.
  5. Duk wanda yayi noma ya huta da awo.
  6. Duk zafin tukunya dole a sauke.
  7. Duk zurfin ruwa akwai yashi a ciki.
  8. Duk tashin tsuntsu, sai sama ta ga bayan shi.
  9. Dutsen tsakiyar ruwa bai san ana rana ba.
  10. Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba.
  11. Duk abinda ka gani a gidan sarki, ya na kasuwa.
  12. Durkusa wa wada ai ba gajiyawa ba ne.
  13. Duniya kamun kifi, kowa ya kamo ya sa a goransa.
  14. Don kai ake hula, har kunne ya samu.
  15. Dan banza yashi ne ko an dunkula shi baya dunkuluwa.
  16. Dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido.
  17. Dan kuka mai jawa uwarsa jifa.
  18. Dan kuka baya zama dan tsamiya Ciwon da kare yayi idan dan akuya ne sai wuka.
  19. Ci naka in ci nawa, ba rowa bane halin zama ne.
  20. Da yayyafi kogi kan cika.
  21. Da tsohuwar zuma ake magani.
  22. Da rarrafe yaro kan tashi.
  23. Da ruwan ciki ake jan na rijiya.
  24. Ciki da gaskiya wuka bata huda shi.
  25. Cin loma yafi jiran malmala.
  26. Barin kashi a ciki baya maganin yunwa.
  27. Biyan bukata yafi dogon buri.
  28. Babban goro sai magogin karfe.
  29. Barawon rakumi daga daddawa ya fara.
  30. Barewa baza ta yi gudu ba danta yayi ra
  31. Babban kaya sai gammo.
  32. Ba’a jan ragama da rigima.
  33. Bakin karen masoyi yafi farin ragon makiyi.
  34. Bakin tukunya mai fidda farin tuwo.
  35. Bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane.
  36. Ba’a maida hannun kyauta baya.
  37. Ba’a yanka karfe sai da karfe.
  38. Baka cin zamanin ka ka ci na wani.
  39. Ba’a kada miya tun dawa na rumbu.
  40. A rashin uwa ake uwar daki.
  41. Ayi wanda za’a yi bera ya zubar da garin kyanwa.
  42. Bani na kashe zomon ba rataya aka bani.
  43. Ba iya kwanciya aka fi kare ba sai dai abun rufa.
  44. Baka do gadon mutun amma kana da gadon batun sa.
  45. Ba ji ba gani auren kurma da makaho.
  46. Ba maraya sai rago.
  47. Ba’a fafe gora ranar tafiya.
  48. A rashin sani kaza ta kwana kan dami.
  49. Ana yi da kai yafi ba’a yi, sarki ya koma mai anguwa.
  50. Ba dan tsayi akan ga wata ba.
  51. Ba domin tuwo akayi ciki ba.
  52. Ana zaton wuta a makera, sai gashi a masaka.
  53. Annurin fuska kaurin hanji.
  54. Ana rabaka da kaya kana nade gammo.
  55. A ruwa ake dadewa ba a wuta ba.
  56. Ana sara ana duban bakin gatari.
  57. Ana bikin duniya ake na kiyama.
  58. Ana ganin wuyan biri ake daureshi a kwankwaso.
  59. A bakin tsoho goro kan tsufa.
  60. A bakin wawa ake jin Magana.
  61. Ba’a sarki biyu a gari daya.
  62. Ba’a shan zuma sai an sha harbi.
  63. Ba’a shan zuma sai da wuta.
  64. Ba’a sayan jaki don a ci sai don daukan kaya.
  65. Ba’a raina zakin gwandan daci don ba’a bata ruwa.
  66. Ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
  67. Ba’a sake wa tuwo suna.
  68. A bari ya huce shi ke kawo rabon wani.
  69. A bar kaza cikin gashinta.
  70. Abin bai dace ba, an ga Malami da gatari.
  71. Abinda babba ya gani a zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai gan shi ba.
  72. Allah Ya fishemu da hawa dokin zuciya.
  73. Abinda ruwan zafi ya dafa, in an hakura, ruwan sanyi ma saiya dafa.
  74. Abinda ya bata a duniya in an je lahira a ganshi.
  75. Abin da ya kori bera ya fada wuta, yafi wutar zafi.
  76. Abin da sake, an bai wa mai kaza kai.
  77. Abin da sake an bai wa mai rogo bawo.
  78. Abin da zuciya ya dauka, gangan jiki ma dole ya dauka.
  79. Abin da baki ya daura, hannu baya kwancewa.
  80. Abin mamaki, mai karfi na bara.
  81. Allah ke ci da maraya ko da mai uba bai so ba.
  82. Allah na taimokon wanda ya taimaki kanshi.
  83. Abokin cin mushe ba’a boye mashi wuka.
  84. Abin fada na mai baki ne.
  85. Abu a rufe mai raba zumunci.
  86. Abu kamar wasa, karamar Magana ta zama babba.
  87. Abu uku su ne maganin zaman duniya, tawakkali, dangana da hakuri.
  88. An daga sama anyi wa wada sata.
  89. Ana babbakar giwa wa ke ta zomo?
  90. Abu namu maganin a kwabe mu.
  91. Abokin kirki ya fi mugun dan uwa.
  92. A dade ana yi sai gaskiya.
  93. A dubi ruwa a dubi tsaki.
  94. Abokin sarki, sarki ne.
  95. Abokin kuka ake gaya wa mutuwa.
  96. A ci baa sayar ba, kwai ya fi doki.
  97. A ci a rage, shi ne ci.
  98. A jefar da kwallon mangwaro a huta da kuda.
  99. A aiki kare ya aiki wutsiya.
  100. Aiki da hankali yafi aiki da agogo.
  101. Aikin banza hutun jaki da kaya.
  102. A kan wanke tukunya domin tuwon gobe.
  103. Allah ke gyara tuwon makauniya har a ci ba kuda ba gashi.
  104. Allura a cikin ruwa mai hikima kan tsinta.
  105. Bari murna karen ka ya kama zaki.
  106. Bashi hanji ne yana cikin kowa.
  107. Allaura a cikin teku mai daukanta sai mai dace.
  108. Alheri gadon bacci ne.
  109. Alheri ne bakon gishiri a shekara ana lashewa.
  110. Alhaki kuykuyo ne mai shi yake bi.
  111. Amfanin sani aiki da shi.
  112. Ba za’a ci kwado da yaro ba sai ya wanke hannunsa.
  113. Da walakin goro a cikin miya.

Conclusion

The above Karin Magana (Hausa proverbs) are at your disposal. Feel free to use them anytime you feel like it. You could also tell us more in the comments section. Thank you.